ABNA24 : Kamfanin dillancin labaran reuters ya bayyana cewa a jiya Alhamis ne ya sami rahoton hukumar ta IAEA dangane da wannan ci gaban, sannan labarin ya kara da cewa an fara amfani da sabbin injunan ne tun ranar 31 ga watan Maris da ya gabata wato ranar Laraban da wuce.
Wannan dai na daga cikin shirin kasar Iran na yin nesa da yarjejeniyar shirinta na makamashin nukliya wacce aka fi sani da JCPOA tun bayan da gwamnatin Amurka ta ficce daga yarjejeniyar a shekara ta 2018 sannan ta dora mata takunkuman tattalin arziki mafi muni a tarihin kasar.
Sabbin injunan dai wato IR-4 su na da karfin tace sinadarin yuranium fiye da wadanda take amfani da su a da.
342/